18 KEHF

 • 18:1

  Gõdiya ta tabbata ga Allah wanda Ya saukar da Littafi a kan bãwansa kuma bai sanya karkata ba a gare shi.

 • 18:2

  Madaidaici, dõmin Ya yi gargaɗi da azãba mai tsanani daga gare shi, kuma Ya yi bushãra ga mũminai, waɗanda suke aikata ayyuka na ƙwarai da (cẽwa) sunã da wata lãdã mai kyau.

 • 18:3

  Sunã mãsu zama a cikinta har abada.

 • 18:4

  Kuma Ya yi gargaɗi ga waɗanda suka ce: "Allah yanã da ɗa."

 • 18:5

  Ba su da wani ilmi game da wannan magana, kuma iyãyensu bã su da shi, abin da ke fita daga bãkunansu ya girma ga ya zama kalmar faɗa! Ba su faɗan kõme fãce ƙarya.

 • 18:6

  To, kã yi kusa ka halaka ranka a gurabbansu, wai dõmin ba su yi ĩmãni da wannan lãbãri ba sabõda baƙin ciki.

 • 18:7

  Lalle ne Mũ, Mun sanya abin da ke kan ƙasa wata ƙawa ce gare ta, dõmin Mu jarraba su; wanne daga cikinsu zai zama mafi kyau ga aiki.

 • 18:8

  Kuma lalle Mũ, Mãsu sanya abin da ke a kanta (ya zama) turɓãya ƙeƙasasshiya ne.

 • 18:9

  Ko kuwa kã yi zaton cẽwa ma'abũta kõgo da allo sun kasance abin mãmãki daga ãyõyin Allah?

 • 18:10

  A lõkacin da samarin suka tattara zuwa ga kõgon, sai suka ce: "Ya Ubangijinmu! Ka bã mu wata rahama daga gare Ka, kuma Ka sauƙaƙe mana (sãmun) shiriya daga al'amarinmu."

 • 18:11

  Sai Muka yi dũka a kan kunnunwansu, a cikin kõgon, shẽkaru mãsu yawa.

 • 18:12

  Sa'an nan Muka tãyar da su, dõmin Mu san wane ɗayan ƙungiyõyin biyu suka fi lissãfi ga abin da suka zauna na lõkacin.

 • 18:13

  Mu ne ke jẽranta maka lãbãrinsu da gaskiya. Lalle ne sũ, waɗansu samãri ne. Sun yi ĩmãni da Ubangijinsu, kuma Muka ƙãra musu wata shiriya.

 • 18:14

  Kuma Muka ɗaure a kan zukãtansu, a lõkacin da suka tsayu, sa'an nan suka ce: "Ubangijinmu Shĩ ne Ubangijin sammai daƙasa. Bã zã mu kirãyi waninSa abin bautawa ba. (Idan mun yi haka) lalle ne, haƙĩƙa, mun faɗi abin da ya ƙẽtare haddi a sa'an nan."

 • 18:15

  "Ga waɗannan mutãnenmu sun riƙi waninSa abin bautãwa! Don me bã su zuwa da wata hujja bayyananna a kansu (waɗanda ake bautawar)? To, wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙãga ƙarya ga Allah?"

 • 18:16

  "Kuma idan kun nĩsance su sũ da abin da suke bautãwa, fãce Allah, to, ku tattara zuwa ga kõgon sai Ubangijinku Ya watsa muku daga rahamarSa kuma Ya sauƙaƙe muku madõgara daga al'amarinku."

 • 18:17

  Kuma kanã ganin rãnã idan ta fito tanã karkata daga kõgonsu wajen dãma kuma idan ta fãɗi tanã gurgura su wajen hagu, kuma su, sunã a cikin wani fili daga gare shi. Wannan abu yanã daga ãyõyin Allah. Wanda Allah Ya shiryar, to shĩ ne mai shiryuwa, kuma wanda Allah Ya ɓatar to bã zã ka sãmar masa wani majiɓinci mai shiryarwa ba.

 • 18:18

  Kuma kanã zaton su farkakku ne, alhãli kuwa sũ mãsu barci ne. Munã jũya su wajen dãma da wajen hagu, kuma karensu yanã shimfiɗe da zirã'õ'in ƙafãfuwansa ga farfãjiya (ta kõgon). Dã ka lẽka (a kan) su (dã) lalle ne, ka jũya daga gare su a guje kuma (dã) lalle ne ka cika da tsõro daga gare su.

 • 18:19

  Kuma kamar wannan ne Muka tãyar da su, dõmin su tambayi jũna a tsakãninsu. Wani mai magana daga cikinsu ya ce: "Mẽne ne lõkacin da kuka zauna?" suka ce: "Mun zauna yini ɗaya ko sãshen yini." Suka ce: "Ubangijinku ne Mafi sani ga abin da kuka zauna. To, ku aika da ɗayanku, game da azurfarku wannan, zuwa ga birnin. Sai ya dũba wanne ne mafi tsarki ga abin dafãwa, sai ya zo muku da abinci daga gare shi. Kuma sai ya yi da hankali, kada ya sanar da ku ga wani mutum."

 • 18:20

  "Lalle ne sũ idan sun kãmã ku, zã su jẽfẽ ku, kõ kuwa su mayar da ku a cikin addininsu kuma bã zã ku sãmi babban rabo, ba, a sa'an nan har abada."

 • 18:21

  Kuma kamar wancan ne, Muka nũna su (gare su) dõmin su san lalle wa'adin Allah gaskiya ne, kuma lalle ne Sa'a bãbu shakka a cikinta. A lõkacin da suke jãyayyar al'amarinsu a tsakãninsu sai suka ce: "Ku gina wani gini a kansu, Ubangijinsu ne Mafi sani game da su." Waɗanda suka rinjãya a kan al'amarinsu suka ce: "Lalle mu riƙi masãllãci a kansu."

 • 18:22

  Zã su ce: "Uku ne da na huɗunsu karensu."Kuma sunã cẽwa, "Biyar ne da na shidansu karensu," a kan jĩfa a cikin duhu. Kuma sunã cẽwa, "Bakwaine da na takwas ɗinsu karensu."Ka ce: "Ubangijĩna ne Mafi saniga ƙidãyarsu, bãbu wanda ya san su fãce kaɗan."Kada ka yi jãyayya bayyananna. Kuma kada ka yi fatawa ga kõwa daga gare su a cikin al'amarinsu.

 • 18:23

  Kuma kada lalle ka ce ga wani abu, "Lalle ni, mai aikatãwa ne ga wancan a gõbe."

 • 18:24

  Fãce idan Allah Ya so. Kuma ka ambaci Ubangijinka idan ka manta, kuma ka ce: "¦ammãni ga Ubangijĩna, Ya shiryar da ni ga abin da yake shi ne mafi kusa ga wannan na shiriya."

 • 18:25

  Kuma suka zauna a cikin kõgonsu shẽkaru ɗarĩ uku kuma suka daɗa tara.

 • 18:26

  Ka ce: "Allah ne Mafi sani ga abin da suka zauna. Shĩ ne da (sanin) gaibin sammai da ƙasa. Mũne ne ya yi ganinSa da jinSa! Bã su da wani majiɓinci baicinSa kuma bã Ya tãrayya da kõwa a cikin hukuncinsa."

 • 18:27

  Ka karanta abin da aka yi wahayi zuwa gare ka, na littãfin Ubangijinka. Bãbu mai musanyãwa ga kalmõminSa kuma bã zã kã sãmi wata madõgara ba daga waninsa.

 • 18:28

  Ka haƙurtar da ranka tãre da waɗanda ke kiran Ubangijinsu, sãfe da maraice, sunã nufin yardarSa. Kuma kada idãnunka su jũya daga barinsu, kanã nufin ƙawar rãyuwar dũniya. Kuma kada ka biwanda Muka shagaltar da zũciyarsa daga hukuncinMu, kuma ya bi son zuciyarsa, alhãli kuwa al'amarinsa ya kasance yin ɓarna.

 • 18:29

  Kuma ka ce: "Gaskiya daga Ubangijinku take." Sabõda haka wanda ya so, to, ya yi ĩmãni, kuma wanda ya so, to, ya kãfirta. Lalle ne Mũ, Mun yi tattali dõmin azzãlumai wata wuta wadda shãmakunta, sun ƙẽwaye da su. Kuma idan sun nẽmi taimako sai a taimake su da wani ruwa kamar dabzar mai, yanã sõye fuskõki. Tir da abin shansu, kuma wutar ta yi mũnin zama mahũtarsu.

 • 18:30

  Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai lalle ne Mũ bã Mu tõzartar da lãdar wanda ya kyautata aiki.

 • 18:31

  Waɗannan sunã da gidãjen Aljannar zama, ƙõramu na gudãna daga ƙarƙashinsu, anã sanya musu ƙawa, a cikinsu, daga mundãye na zinariya, kuma sunã tufantar waɗansu tũfãfi kõre, na alharĩni raƙĩƙi da alharini mai kauri sunã kishingiɗe a cikinsu, a kan, karagu. Mãdalla da sakamakonsu. Kuma Aljanna ta kyautatu da zama wurin hutãwa.

 • 18:32

  Kuma ka buga musu misãli da waɗansu maza biyu. Mun sanya wa ɗayansu gõnaki biyu na inabõbi, kuma Muka kẽwayesu da itãcen dabĩnai, kuma Muka sanya shũka a tsakãninsu (sũ gõnakin).

 • 18:33

  Kõwace gõna daga biyun, tã bãyar da amfãninta, kuma ba ta yi zãluncin kõme ba daga gare shi. Kuma Muka ɓuɓɓugar da ƙoramu a tsakãninsu.

 • 18:34

  Kuma ɗan ĩtãce ya kasance gare shi. Sai ya ce wa abõkinsa, alhali kuwa yanã muhãwara da shi, "Nĩ ne mafĩfĩci daga gare ka a wajen dũkiya, kuma mafi izza a wajen jama'a."

 • 18:35

  Kuma ya shiga gõnarsa, alhãli yanã mai zãlunci ga kansa, ya ce: "Bã ni zaton wannan zã ta halaka har abada."

 • 18:36

  "Kuma bã ni zaton sa'a mai tsayuwa ce, kuma lalle ne, idan an mayar da ni zuwa ga Ubangijiĩna, to, lalle ne, zan sãmi abin da yake mafi alhẽri daga gare ta ya zama makõma."

 • 18:37

  Abõkinsa ya ce masa, alhãli kuwa yanã muhãwara da shi, "Ashe kã kãfirta da wanda Ya halitta ka daga turɓaya, sa'an nan daga ɗigon maniyi, sa, an nan Ya daidaita ka, ka zama mutum?"

 • 18:38

  "Amma ni, shĩ ne Allah Ubangijina, kuma bã zan tãra kõwa da Ubangijina ba"

 • 18:39

  "Kuma don me, a lõkacin da ka shiga gõnarka, ka, ce, 'Abin da Allah ya so (shi ke tabbata) bãbu wani ƙarfi fãce game da Allah.' Idan ka gan ni, ni ne mafi ƙaranci daga gare ka a wajen dũkiya da ɗiya."

 • 18:40

  "To, akwai fãtan Ubangijĩna Ya ba ni abin da yake mafi alhẽri daga gõnarka, kuma ya aika azãba a kanta (ita gõnarka) daga sama, sai ta wãyi gari turɓãya mai santsi."

 • 18:41

  "Kõ kuma ruwanta ya wãyi gari faƙaƙƙe, sabõda haka, bã zã ka iya nẽmo shi ba dõminta."

 • 18:42

  Kuma aka halaka dukan 'ya'yan itãcensa, sai ya wãyi gari yanã jũyar da tãfunansa biyu, sabõda abin da ya kashe a cikinta, alhãli kuwa ita tanã kwance a kan rassanta, kuma yanã cẽwa, "Kaitõna, dã dai ban tãra wani da Ubangijina ba!"

 • 18:43

  Kuma wata jama'a ba ta kasance a gare shi ba, waɗanda ke taimakon sa, baicin Allah, kuma bai kasance mai taimakon kansa ba.

 • 18:44

  A can taimako da jiɓinta ga Allah yake. Shĩ ne kawai Gaskiya, shĩ ne Mafĩfĩci ga lãda kumaMafĩ fĩci ga ãƙiba.

 • 18:45

  Ka buga musu misãlin rãyuwar dũniya, kamar ruwane wanda Muka saukar da shi daga sama sa'an nan tsirin ƙasa ya garwaya da shi, sa'an nan ya wãyi gari dudduga, iska tanã shiƙar sa. Kuma Allah Ya kasance Mai yawan ĩkon yi ne a kan dukan kõme.

 • 18:46

  Dũkiya da ɗiya, sũ ne ƙawar rãyuwar dũniya, kuma ayyuka mãsu wanzuwa na ƙwarai sun fi zama alhẽri a wurin Ubangijinka ga lãda kuma sun fi alhẽri ga bũri.

 • 18:47

  Kuma a rãnar da Muke tafiyar da duwãtsu, kuma ka ga ƙasa bayyane, kuma Mu tãra su har ba Mu bar kõwa ba daga gare su.

 • 18:48

  Kuma a gittã su ga Ubangijinka sunã sahu guda, (Mu ce musu), "Lalle ne haƙĩƙa kun zo Mana, kamar yadda Muka halitta ku a farkon lõkaci. Ã'a, kun riya cẽwa bã zã Mu sanya mukuwani lõkacin haɗuwa ba."

 • 18:49

  Kuma aka aza littãfin ayyuka, sai ka ga mãsu laifi sunã mãsu jin tsõro daga abin da ke cikinsa, kuma sunã cẽwa "Kaitonmu! Mẽne ne ga wannan littãfi, bã ya barin ƙarama, kuma bã ya barin babba, fãce yã ƙididdige ta?" Kuma suka sãmi abin da suka aikata halarce. Kuma Ubangijinka bã Ya zãluntar kõwa.

 • 18:50

  Kuma a lõkacin da Muka ce wa malãiku, "Ku yi sujada ga Ãdamu." Sai suka yi sujada fãce Iblĩsa, yã kasance daga aljannu sai ya yi fãsiƙanci ga barin umurnin Ubangijinsa, To fa, ashe, kunã riƙon sa, shi da zũriyarsa, su zama majiɓinta baicin Ni, alhãli kuwa su maƙiya ne a gare ku? Tir da ya zama musanya ga azzãlumai.

 • 18:51

  Ban shaida musu halittar sammai da ƙasa ba, kuma ban (shaida musu) halittar rãyukansu ba kuma ban kasance mai riƙon mãsu ɓatarwa (da wani) su zama mataimaka ba.

 • 18:52

  Kuma da rãnar da Allah Yake cẽwa, "Ku kirãyi abõkan tarayyãTa, waɗanda kuka riya." Sai su kirãye su, sai bã zã su karɓa musu ba, kuma Mu sanya Maubiƙa (Mahalaka) a tsakãninsu,

 • 18:53

  Kuma mãsu laifi suka ga wutã suka tabbata lalle ne, sũ mãsu, auka mata ne, kuma ba su sãmi majũya ba daga gare ta.

 • 18:54

  Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun jujjũya, a cikin wannan Alƙur'ãni, daga kõwane irin misãli ga mutãne (dõmin su gãne, su bi sharĩ'a), kuma mutum yã kasance mafi yawan abu ga jidãli.

 • 18:55

  Kuma bãbu abin da ya hana mutãne su yi ĩmãni a lõkacinda shiriya ta zo musu, kuma su nẽmi gãfara daga Ubangijinsu, fãce hanyar farko ta je musu kõ kuma azãba ta jẽ musu nau'i-nau'i.

 • 18:56

  Kuma ba Mu aika Manzanni ba fãce sunã mãsu bãyar da bushãra kuma mãsu gargaɗi, kuma waɗanda suka kãfirta sunã jidãli da ƙarya dõmin su ɓãta gaskiya da ita, kuma suka riƙi ãyõyiNa da abin da aka yi musu gargaɗi da shi abin izgili.

 • 18:57

  Kuma wãne ne mafi zãlunci daga wanda aka tunãtar game da ãyõyin Ubangijinsa, sai ya bijire daga barinsu, kuma ya manta abin da hannãyensa suka gabãtar? Lalle ne Mũ, Mun sanya abũbuwan rufi a kan zukãtansu dõmin kada su fahimcẽ shi, kuma a cikin kunnuwansu (Mun sanya) wani nauyi, kuma idan kã kĩrayẽ su zuwa ga shiriya, to, bã zã su shiryu ba, a sa'an nan, har abada.

 • 18:58

  Kuma Ubangijinka Mai gãfara ne, Ma'abũcin rahama. Dã Yanã kãma su sabõda abin da suka sanã'anta, lalle ne, dã Ya gaggauta azãba a gare su. Ã'a, sunã da lõkacin alkawari, (wanda) bã zã su sãmi wata makõma ba, baicinSa.

 • 18:59

  Kuma waɗancan alƙaryu Mun halaka su, a lõkacin da suka yi zãlunci, kuma Muka sanya lõkacin alkawarin, ga halaka su.

 • 18:60

  Kuma a lõkacin da Mũsã ya ce wa yãronsa, "Bã zan gushe ba sai na isa mahaɗar tẽku biyu, kõ in shũɗe da tafiya shekara da shẽkaru."

 • 18:61

  To, a lõkacin da suka isa mahaɗar tsakãninsu sai suka manta kĩfinsu, sai ya kãma tafarkinsa a cikin tẽku kamar bĩga.

 • 18:62

  To, a lõkacin da suka wuce ya ce wa yãronsa, "Ka kãwo mana kãlãcinmu. Lalle ne haƙĩƙa mun haɗu da wahala daga tafiyarmu wannan."

 • 18:63

  (Yãron) ya ce: "Kã gani! A lõkacin da muka tattara zuwa ga falalen nan to, lalle nĩ, na manta kĩfin, kuma bãbu abin da yamantar da nĩ shi, fãce Shaiɗan, dõmin kada in tuna shi, sai ya kama tafarkinsa a cikin tẽku, da mãmãki!"

 • 18:64

  Ya ce: "Wancan ne abin da muka kasance munã biɗã." Sai suka kõma a kan gurãbunsu, sunã bĩbiya.

 • 18:65

  Sai suka sãmi wani bãwa daga bãyinMu, Mun bã shi wata rahama daga wurinMu, kuma Mun sanar da shi wani ilmi daga gunMu.

 • 18:66

  Mũsã ya ce masa, "Ko in bĩ ka a kan ka sanar da ni daga abin da aka sanar da kai na shiriya?"

 • 18:67

  Ya ce: "Lalle ne kai bã zã ka iya yin haƙuri tãre da nĩ, ba."

 • 18:68

  "Kuma yãya zã ka yi haƙuri a kan abin da ba ka kẽwayeda shi ba ga jarrabãwa?"

 • 18:69

  Ya ce: "Za ka sãme ni, in Allah Yã so mai haƙuri kuma bã zan sãɓa maka ba ga wani umurni."

 • 18:70

  Ya ce: "To idan ka bĩ ni to kada ka tambaye ni daga kõme sai na lãbarta maka ambato daga gare shi."

 • 18:71

  Sai suka tafi har a lõkacin da suka hau a cikin jirgi, ya hũje shi, ya ce, "Kã hũje shi dõmin ya nutsar da mutãnensa? Lalle ne, haƙĩƙa, kã zo da wani babban abu!"

 • 18:72

  Ya ce: "Ashe ban ce, lalle kai, bã za ka iya yin haƙuri tãre da ni ba?"

 • 18:73

  Ya ce: "Kada ka kãma ni da abin da na manta kuma kada ka kallafa mini tsanani ga al'amarĩna."

 • 18:74

  Sai suka tafi, har suka haɗu da wani yãro, sai ya kashe shi. Ya ce: "Ashe kã kashe rai tsarkakakke, bã da wani rai ba? Lalle ne haƙĩƙa ka zo da wani abu na ƙyãma."

 • 18:75

  Ya ce: "Shin, ban ce maka ba, lalle ne kai bã zã ka iya yin haƙuri tãre da nĩ ba?"

 • 18:76

  Ya ce: "Idan na tambaye ka daga wani abu a bãyanta, to, kada ka abũce ni. Lalle ne, kã isa ga iyakar uzuri daga gare ni."

 • 18:77

  Sai suka tafi, har a lõkacin da suka je wa mutãnen wata alƙarya, suka nẽmi mutãnenta da su bã su abinci, sai suka ƙi su yi musu liyãfa. Sai suka sãmi wani bango a cikinta yanã nufin ya karye, sai (Halliru) ya tãyar da shi mĩƙe. (Mũsã) ya ce: "Dã kã so, lalle ne dã kã karɓi ijãra a kansa."

 • 18:78

  Ya ce: "Wannan shi ne rabuwar tsakanina da tsakaninka. Zã ni gaya maka fassarar abin da ba ka iya yin haƙuri ba a kansa."

 • 18:79

  "Amma Jirgin, to, ya zama na waɗansu matalauta ne sunã aiki a cikin tẽku, sai na yi niyyar in aibanta shi, alhãli kuwa wani sarki ya kasance a gaba gare su, yanã karɓẽwar kõwane jirgi (lãfiyayye) da ƙwãce.

 • 18:80

  "Kuma amma yaron, to, uwãyensa sun kasance mũminai, to, sai muka ji tsõron ya kallafa musu kangara da kãfirci."

 • 18:81

  "Sai muka yi nufin Ubangijinsu Ya musanya musu mafi alhẽri daga gare shi ga tsarkakuwa, kuma mafi kusantar tausayi."

 • 18:82

  "Kuma amma bangon, to, yã kasance na waɗansu yãra biyu ne, marãyu a cikin birnin, kuma akwai wata taska tãsu a ƙarƙashinsa, kuma ubansu ya kasance sahĩhin mutum ne, dõmin haka Ubangijinka Ya yi nufin su isa iyãkar ƙarfinsu, kuma sũ, su fitar da taskarsu, sabõda rahama ne daga Ubangijinka. Kuma ban yi shi ba daga umurnĩna. Wancan shĩ ne fassarar abin da ba ka iya yin haƙuri ba a kansa."

 • 18:83

  Kuma suna tambayar ka daga zulƙarnaini, ka ce: "Zan karanta muku ambato daga gare shi."

 • 18:84

  Lalle ne Mũ Mun bã shi mulki a cikin ƙasa kuma Muka bã shi daga kõwane abu, hanya (zuwa ga murãdinsa).

 • 18:85

  Sai ya bi hanya.

 • 18:86

  Har a lõkacin da ya isa ga mafãɗar rãnã, kuma ya sãme ta tanã ɓacẽwa a cikin wani ruwa mai baƙar lãkã, kuma ya sãmi waɗansu mutãne a wurinta. Muka ce: "Yã Zulƙarnaini imma dai ka azabtar kuma imma ka riƙi kyautatãwa a cikinsu."

 • 18:87

  Ya ce: "Amma wanda ya yi zãlunci, to zã mu azabta shi, sa'an nan a mayar da shi zuwa ga Ubangijinsa, sai kuma Ya yi masa azãba, azãba abar ƙyãma."

 • 18:88

  "Kuma amma wanda ya yi ĩmãni kuma ya aikata aikin ƙwarai to, zã mu yi sakamako a gare shi (watau kyauta) mai kyau, kuma zã mu gaya masa sauƙi daga umurninmu."

 • 18:89

  Sa'an nan kuma ya bi hanya.

 • 18:90

  Har a lõkacin da ya isa ga mafitar rãnã, ya sãme ta tanã fita a kan waɗansu mutãne (waɗanda) ba Mu sanya musu wata kãriya ba daga barinta.

 • 18:91

  Kamar wancan alhãli kuwa haƙĩƙa, Mun kẽwaye da jarrabãwa ga abin da ke gunsa.

 • 18:92

  Sa'an nan kuma ya bi hanya.

 • 18:93

  Har a lõkacin da ya isa a tsakãnin duwãtsu biyu, ya sãmi waɗansu mutãne daga gabãninsu. Ba su yi kusa su fahimci magana ba.

 • 18:94

  Suka ce: "Yã Zulƙarnaini! Lalle ne Yãjũja da Majũja mãsu ɓarna ne a cikin ƙasa. To, ko zã mu Sanya harãji sabõda kai, a kan ka sanya wani danni a tsakãninmu da tsakãninsu?"

 • 18:95

  Ya ce: "Abin da Ubangijĩna Ya mallaka mini, a cikinsa yã fi zama alhẽri. Sai ku taimakeni da ƙarfi, in sanya babbar katanga a tsakãninku da tsakãninsu."

 • 18:96

  "Ku kãwo mini guntãyen baƙin ƙarfe". (Suka kai masa) har a lõkacin da ya daidaita a tsakãnin duwãtsun biyu (ya sanya wutã a cikin ƙarfen) ya ce: "Ku hũra (da zugãzugai)." Har a lõkacin da ya mayar da shi wutã, ya ce: "Ku kãwo mini gaci (narkakke) in zuba a kansa."

 • 18:97

  Dõmin haka bã za su iya hawansa ba, kuma bã zã su iya hujẽwa gare shi ba.

 • 18:98

  Ya ce: "Wannan wata rahama ce daga Ubangijĩna. Sai idan wa'adin Ubangijĩna ya zo, ya mayar da shi niƙaƙƙe. Kuma wa'adin Ubangijĩna ya kasance tabbatacce."

 • 18:99

  Kuma Muka bar sãshensu a rãnar nan, yanã garwaya a cikin sãshe, kuma aka bũsa a cikin ƙaho sai muka tãra su, tãrãwa.

 • 18:100

  Kuma Muka gitta Jahannama, a rãnar nan ga kãfirai gittãwa.

 • 18:101

  Waɗanda idãnunsu suka kasance a cikin rufi daga tunã Ni, kuma sun kasance bã su iya saurãrãwa.

 • 18:102

  Shin fa, waɗanda suka kãfirta sun yi zaton (daidai ne) su riƙi waɗansu bãyĩNa, majiɓinta baiciNa? Lalle ne, Mun yi tattalin Jahannama ta zama liyãfa ga kãfirai.

 • 18:103

  Ka ce: "Kõ mu gaya muku game da mafĩfita hasãra ga ayyuka?"

 • 18:104

  "Waɗanda aikinsu ya ɓace a cikin rãyuwar dũniya, alhãli kuwa sunã zaton lalle ne sũ, sunã kyautata, (abin da suke gani) aikin ƙwarai?"

 • 18:105

  Waɗancan ne waɗanda suka kãfirta da ãyõyin Ubangijinsu, da kuma haɗuwa da Shi, sai ayyukansu suka ɓãci. Sabõda haka bã zã Mu tsayar musu da awo ba a Rãnar ¡iyãma.

 • 18:106

  Wancan ne sakamakonsu shĩ ne Jahannama, sabõda kãfircinsu, kuma suka riƙi ãyõyiNa da ManzanniNa abin izgili.

 • 18:107

  Lalle ne, waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, Aljannar Firdausi ta kasance ita ce liyãfa a gare su.

 • 18:108

  Suna madawwama a cikinta, bã su nẽman makarkata daga barinta.

 • 18:109

  Ka ce: "Dã tẽku ta kasance tawada ga (rubũtun) kalmõmin Ubangijina, lalle ne dã tẽkun ta ƙãre a gabãnin kalmõmin Ubangijĩna su ƙãre, kuma kõda mun jẽ da misãlinsa dõmin ƙari."

 • 18:110

  Ka ce: "Nĩ, mutum ne kawai kamarku, anã yin wahayi zuwa gare ni cewa: Lalle ne, Abin bautawarku, Abin bautawa Guda ne, sabõda haka wanda ya kasance yanã fãtan haɗuwa da Ubangijinsa, to, sai ya yi aiki na ƙwarai. Kuma kada ya haɗa kõwa ga bauta wa Ubangijinsa."

Paylaş
Tweet'le